An yi jana'izar Dan Ibro

Hakkin mallakar hoto Dan Ibro Facebook
Image caption Dan Ibro ya rasu ne sanadiyar ciwon koda, a cewar makusantansa

An yi jana'izar fitaccen dan wasan kwaikwayon hausa, Rabilu Musa Dan Ibro a garinsu mai suna Danlasan da ke jihar Kano a Najeriya.

Dan Ibro ya rasu ne da safiyar ranar Laraba.

Wani amininsa, Falalu Dorayi ya shaida wa BBC cewa Dan Ibro ya rasu ne sakamakon ciwon koda.

Dan wasan dai ya yi fice musamman a wasannin barkwanci.