Dan wasan Hausa, Rabilu Dan Ibro ya rasu

Ibro ya yi fice a wasannin ban-dariya
Bayanan hoto,

Ibro ya yi fice a wasannin ban-dariya

Shahararren dan wasan kwaikwayon Hausa, Rabilu Musa, wanda aka fi sani da Dan Ibro ya rasu.

Wani fitaccen dan wasan, kuma aminin Dan Ibro, Falalu Dorayi ya shaida wa BBC cewa Dan Ibro ya rasu ne da safiyar ranar Laraba.

A cewarsa, Dan Ibro ya rasu ne sakamakon ciwon koda.

Dan wasan dai ya yi fice musamman a wasannin barkwanci.