Shafin Instagram ya shiga gaban Twitter

Image caption Instagram yana da masu amfani da shi miliyan 3

Shafin sada zumunci da hotuna na Instagram ya ce yana da damar sauya yadda harkoki ke gudana a duniya, yayin da ya ce ya shiga gaban Twitter da yawan masu amfani da shi miliyan 3.

Shugaban Instagram, Mr. Kevin Systrom ya bayyana habbakar da shafin yake yi da cewa abin farin ciki ne, sannan ya ce shafin zai cigaba da bunkasa.

Shafin Twitter ya ce kimanin mutane miliyan 284 ne ke amfani da shi a kowanne wata.

Shafin Facebook wanda ke bugun kirji yanada mutane biliyan 1 da miliyan 350 masu amfani da shi a kowanne wata, ya saye Instagram a shekarar 2012.

Shugaban Instagram, Mr. Systrom ya shaidawa kafar yada labarai ta Newsbeat cewa "manufar shafin Instagram ita ce sanin mai duniyar take ciki nan take, ba kawai daukan hoton kyakkyawan yaro ko kare ba''.

Shafin na Instagram zai bullo da tsarin tantance shafukan mutane na hakikani, da za a sa musu alama mai ruwan bula kamar yadda yake a shafukan Facebook da Twitter.

Hakkin mallakar hoto facebook
Image caption Shafin Facebook ya saye Instagram a 2012

Mr. Systrom ya ce "muna so ne dukkan masu amfani da shafinmu su zamo mutane ne na hakikani, domin tabbatar da babu wanda yake mu'amala da butun-butumi''.

Ya ce a kokarin da Instagram ya ke na kawar da shafukan bogi, da masu karya ka'idojin kamfanin, shafin ya fara rufe shafukan wasu.

Tunda Kevin Systrom da Mike Krieger suka samar da shafin Instagram a 2010, shafin ya habbaka cikin sauri.

A watan Fabuwairun 2013, kamfanin ya sanar da cewa masu amfani da shi sun kai mutane miliyan 100.

A watan Yunin 2014, shafin Instagram ya kare matakin da ya dauka na cire hotunan matan da suka bar kirjinsu a bude daga shafukansu.