Boko Haram: An kashe mutane 6 a Kano

Hakkin mallakar hoto Habibu Yahaya
Image caption Kasa da makonni biyu kenan da aka kai wani mummunan hari a masallacin juma'a a jihar ta Kano

Rundunar 'yan sandan Kano ta ce mutane shida ne suka mutu a harin kunar bakin wake da wasu mata biyu suka kai Kantin kwari.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Adenerele Shinaba ya ce mutane shidan sun hada da 'yan kunar bakin waken biyu, yayin da wasu mutane bakwai kuma suka jikkata.

Sai dai wasu na cewa yawan wadanda lamarin ya shafa ya dara hakan.

A dai kai harin ne a filin fakin inda ake loda kaya a cikin motoci, lamarin da yasa kasuwar ta yamutse yayin da mutane ke kokarin tsira da ransu.

Kasuwar Kantin Kwari ita ce kasuwa mafi girma da ake sayar da tufafi a jihar kuma mutane daga wasu sassan Najeriya da ma wasu kasashe na zuwa cin kasuwar.

A watan da ya gabata ne, aka kai hari a babban masallacin gidan sarkin Kano, lamarin da ya janyo rasuwar mutane fiye da 100.

Jihar ta Kano dai ta sha fuskantar hare-haren kungiyar Boko Haram a baya.