Mata sun yi karar gwamnatin Kenya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Matan suna kira da a dakatar da al'adar juyar da mahaifa

Wasu mata masu dauke da kwayar cutar HIV a Kenya sun shigar da gwamnatin kasar kara suna zarginta da tilasta musu juyar da mahaifa.

Matan su biyar suna neman diyya daga gwamnati da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suke zargi da hannu wajen juyar musu da mahaifa.

Matan dai sun yi zanga-zangar lumana a gaban kotun bayan sun shigar da karar.

A kasar a shekarar 2012 wata kotu a Namibia ta yanke hukuncin cewa an tilasta wa wasu mata uku masu HIV juyar da mahaifa.