Jonathan bai iya mulki ba - Obasanjo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani na hannun shugaba Jonathan Kashamu Buruji ne ya shigar da kara don a dakatar da kaddamar da littafin

Tsohon shugaban Nigeria, Cif Olusegun Obasanjo ya kaddamar da littafi kan tarihin rayuwarsa, inda a ciki ya bayyana shugaba Goodluck Jonathan da cewa bai iya mulki ba.

Obasanjo ya kaddamar da littafin My Watch a jihar Lagos a ranar Talata duk da umarnin da wata kotu a kasar ta bayar na cewa ya dakatar da kaddamarwar.

Tsohon shugaban ya ce "Bayan na yi nazarinsa na kuma yi kokarin yi masa magana, kana na saurari shugaban kasar da kansa da kuma mutanen da ke kewaye da shi, abin bakin ciki na cimma matsayi guda cewa Jonathan mutum ne da ba shi da cikakkiyar basirar da zai jagoranci Nigeria."

A littafin Obasanjo ya bayyana Jonathan da cewa shugaba ne wanda zai iya sadaukar da komai da kowa da ya dauka ba su da muhimmanci domin ya cimma burinsa na kashin kansa.

Wasu hujjojinsa

Obasanjo ya bayar da misali da cewa, lokaci ma fi tsawo da ya shafe da shugaban kasar shi ne sa'a guda da mintoci goma "Kuma a tsawon wannan lokacin, shugaban kasar bai furta wata magana da ta shafi kasa ba, sai maganar su waye makiyansa da kuma abubuwan da ba su zo daidai da abin da yasa a gaba ba".

Haka kuma Obasanjo ya ce shugaba Jonathan bai damu da komai ba face ya ci gaba da kasancewa a kan mulki.

Inda nan ma ya ba da misali da alkawarin da Jonathan ya yi na yin wa'adin mulki daya, amma bayan zaben 2011 sai ga shi ya ci gaba da kulla-kullar yadda zai zarce wa'adi na biyu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dangantaka ta yi tsami tsakanin Obasanjo da Jonathan

Wani batu kuma da littafin ya tabo game da shugaba Jonathan shi ne batun cin hanci da rashawa, wanda ya ce ya yi wa gwamnati katutu.

Obasanjo ya kuma bayyana cewa wani dattijo da yake da kusanci da shugaba Jonathan a watanni shida na farkon mulkinsa ya gaya masa cewa ya yi kokarin fadakar da Jonathan cewa shugabanni biyar ne a Najeriya.

"Mai dakin shugaban kasa da Diezani (Alison Madueke) da Stella(Oduah) da Ngozi (Iweala) sai kuma shugaban kasar da kansa kuma shi ne mafi rauni a cikinsu."

Atiku da El-Rufa'i

Cif Obasanjo bai tsaya kan Jonathan kadai ba, littafin nasa ya kuma bayyana tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar da cewa tsabagen makaryaci ne, kana ya bayyana tsohon ministan Abuja Nasir El-Rufa'i da cewa yana da basira, amma shi ma makaryaci ne.

Sai kuma tsohon gwamnan jihar Legas Bola Ahmed Tinubu wanda Obasanjo ya ce cin hanci da rashawa sun yi masa kanta.