Pistorius: An amince a daukaka kara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A watan Fabrairun 2012 ne, Oscar Pistorius, ya harbe budurwarsa Reeva Steenkamp a bandaki

Wata mai shari'a a Afrika ta Kudu ta amince masu gabatar da kara su daukaka kara kan hukuncin da ta yanke wa zakaran tseren wasan nakasassun nan Oscar Pistorius.

Za a daukaka karar zuwa kotun kolin kasar, inda masu shigar da kara za su nemi a yanke masa hukunci kan kisan kai da gangan.

A watan Octoba ne dai mai shari'a Thokozile Masipa ta ce ba za ta amince a daukaka kara game da hukuncin shekaru biyar a gidan kaso da ta yanke wa Pistorius ba.

Babban mai gabatar da kara Gerrie Nel ya shaida wa kotun cewa hukuncin ya ba da mamaki domin bai da ce ba kwata-kwata.