APC: An soma rarrabe kuri'un 'yan takara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption APC na kokarin kwace mulki a hannun PDP

An soma rarrabe kuri'un da aka kada a zaben fitar da gwani na jam'iyyar adawa ta APC a Nigeria wanda ke gudana a birnin Lagos.

'Ya'yan jam'iyyar APC su 7,214 ne suka kada kuri'a domin zaben mutumin da zai fafata da Shugaba Jonathan na PDP a zaben shugaban kasa na 2015.

Mutanen da ke neman tikitin jam'iyyar ta APC su ne; Janar Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso da Rochas Okorocha da kuma Sam Nda-Isaiah.

Kawo yanzu komai na tafiya cikin kwanciyar hankali da lumana a filin wasa na Teslim Balogun da ake rarrabe kur'iun da kowanne dan takara ya samu.

Duk wanda ya samu nasara zai fuskanci babban kalubale daga jam'iyyar PDP wacce ke mulkin Nigeria tun daga shekarar 1999.