Buhari ne dan takarar APC a 2015

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Janar Buhari na jinjinawa magoya bayansa

Tsohon Shugaban mulkin soja a Nigeria, Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben fitar da gwani domin zama dan takarar jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2015.

Janar Buhari ya samu nasara a kan 'yan takara hudu da suka nemi tikitin na jam'iyyar adawa ta APC, inda aka kwana ana kada kuri'a a filin wasa na Teslim Balogun da ke birnin Lagos.

Wannan zai kasance karo na hudu da Janar Buhari zai yi takarar shugabancin Nigeria, bayan da ya sha kaye a zaben da aka yi a 2003 da 2007 da kuma 2011.

Kuri'un da aka kada:

  • Muhammed Buhari = 3430
  • Rabiu Kwankwaso = 974
  • Atiku Abubakar = 954
  • Rochas = 624
  • Sam Nda-Isaiah = 10

Buhari ya doke Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso da Rochas Okorocha da kuma Sam Nda Isaiah.

Wannan nasarar ta sa Buhari zai ja-zare tsakaninsa da Shugaba Goodluck Jonathan a zaben shugaban kasa da zai gudana a watan Fabarairun 2015.

Jam'iyyar PDP ce ke mulkin Nigeria tun daga shekarar 1999 da kasar ta koma bin tafarkin mulkin demokradiyya.

'Yan adawa na zargin gwamnatin Jonathan da kasa yin abin da ya dace domin murkushe ayyukan 'yan Boko Haram wadanda suka kashe dubban mutane da kuma raba mutane fiye da miliyan daya da muhallansu.