Amare 100 sun bace a China

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mazauna yankunan karkara a China sun gwammace su auri wata daga kasar waje saboda tsadar auren 'yar China

'Yan sanda a kasar China sun ce suna bincike kan batan dabon da wasu amare fiye da dari suka yi a wasu kauyuka da ke arewacin kasar.

An rasa inda amaren 'yan kasar Vietnam suka shiga ne, bayan sun auri wasu mazauna kauyukan a China.

Shi ma kawalin da ya tallata amaren ga mazajen a kan kudi dala 16,000 kowaccensu ya gudu.

Wani jami'i a lardin ya shaida wa wata kafar yada labarai ta kasar cewa, akwai yiwuwar sa hannun gungun masu aikata manyan laifuka a lamarin.