An kai hare-haren bam a Jos

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A cikin wata Mayu an kai harin bam a Jos

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Nigeria na cewa an samu fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton bama-bamai ne.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Alhamis da almuru a yankin Terminus.

Babu dai cikakkun bayanai kan hasarar da bama-baman suka haddasa, amma wasu ganau sun shaida wa BBC cewa sun kirga a kalla gawawwakin mutane talatin.

Kawo yanzu ana aikin kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su.

Hukumomin tsaro ba su ce komai ba kan lamarin.