An samu tashin bama bamai a Jos

Jos Hakkin mallakar hoto
Image caption Ganau sun ce sun ga gawawwarkin mutane da dama a wajen da bama baman suka tashi

Rahotanni daga Jos babban birnin jihar Filato a Najeriya na cewa an samu fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton bama-bamai ne.

Lamarin ya faru ne dazu da almuru a yankin Terminus.

Babu dai cikakkun bayanai kan hasarar da bama-baman suka haddasa, amma wasu ganau sun shaida wa BBC cewa sun kirga akalla gawawwakin mutane talatin baya ga wadanda suka jikkata.

Ana dai kan aikin kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su Kuma yanzu babu wani bayani daga hukumomin tsaro kan lamarin.