Facebook zai kara sabuwar alama a shafinsa

Image caption Masu amfani da facebook na bukatar ganin an kara alamar 'dislike'

Shafin sada da zumunta da muhawara na Facebook na tunanin kara wata alama a shafin ta nuna rashin gamsuwa wato 'dislike' a turance, in ji Mark Zuckerberg

Yayinda yake amsa tambayoyi a birnin California na kasar Amurka, Mark Zuckerberg wanda ya kirkiro da shafin facebook ya ce wannan na daya daga cikin abubuwan da masu amfani da shafin suka fi bukatar ganin an yi.

Ya ce dole ne shafin ya bincika wata hanya domin tabbatar da cewa hakan kuma bai zamo wata hanya da za'a muzanta abinda wani ya rubuta a shafin ba.

Alkaluman Facebook sun nuna cewa ana samun wadanda suka nuna gamsuwarsu wato 'Likes' a turance game da wani abu da aka rubuta a shafin har sau biliyan 4.5 a kowacce rana.

Hakkin mallakar hoto Facebook

Mutumin da ya kirkiro da shafin na facebook ya kara da cewa a mafiyawancin lokuta mutane na bayyana wani abu ga sauran jama'a a shafin facebok na irin lokutan bakin ciki da suka shiga a rayuwarsu.

'Saboda haka a wasu lokuta mutane na fada mana cewa basa jin dadi su ga cewa sun danna alamar gamsuwa ko kuma 'like' a turance game da wannan abu' in ji Zuckerberg

Ya kara da cewa wasu mutane sun nemi a kara wannan alama ta nuna rashin gamsuwa wato 'dislike' a turance saboda su na son su ce abin da aka rubuta ba mai kyau bane, abu ne da muke ganin ba shi bane alheri ga duniya'