An yi wa 'yar shekaru uku fyade a Kaduna

A ci gaba da samun matsalar fyade a Najeriya, an tsinci gawar wata yarinya 'yar kimanin shekara ukku a Kaduna wacce aka yi wa fyade har sai da ta rasu.

Rahotanni dai na nuna cewa yarinyar ta fita daga gidan su ne zuwa gidan kakanta dake kusa.

Matsalar fyade matsala ce wacce ta ki ci taki cinyewa a Najeriya.

Yayin da wasu ke cewa ya kamata a samar da horo mai tsanani, wasu na cewa ya kamata iyaye su kara kula da 'ya'yansu.