Ghana zata rufe sansanonin tsare Mayu

Hakkin mallakar hoto CFL
Image caption kimanin mata 600 ne ake tsare da su a Ghana bisa zargin maita

A kasar Ghana, gwamnati ta tsayar da ranar 15 ga watan Disamba domin fara rufe sansanoni 6 da ake tsare da wasu mutane bisa zarginsu da maita.

Hukumomin kasar sun cimma wannan matakin ne a wajen wani taro da jami'an ma'aikatar harkokin mata da yara kanana tare da wasu kungiyoyin kare hakkin bil Adama da suka hada da Action Aid a Accra.

An kafa sansanonin ne shekaru da yawa da suka wuce.

Kimanin mata 600 masu kimanin shekaru 60 ne ake tsare da su a sansanonin.

Ministar harkokin mata da yara kanana a Ghana ta ce bai kamata a cigaba da tsare matan ba batare da an tabbatar da abun dake damun suba, inda tace ana cin zarafinsu a wasu lokutan.