Jos: 'Talakawa na bukatar kariya a Nigeria'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta hallaka dubban talakawa a Nigeria

Archbishop na Jos a tsakiyar Nigeria ya ce bukaci mahukunta a kasar su kara kaimi wajen kare talakawa daga fuskantar hare-hare.

Ya bayyana haka ne kwana guda bayan an kashe mutane a kalla 30 a harin tagwayen bama-bamai a kusa da kasuwar Terminus ta Jos.

Archbishop Ben Kwashi ya shaida wa BBC cewa galibin wadanda hare-haren ke rutsawa da su talakawa ne wadanda ba za su iya kare kansu ba.

Ana zargin kungiyar Boko Haram da kai hare-hare kan fararen hula a Nigeria.

Sai dai limamin cocin ya ce maharan ba za su yi nasarar janyo tashin hankalin addinni ba, a birnin da ke da tarihin rikicin addinni da kabilanci.

A watan Mayu an kai hari a birnin Jos, lamarin da ya janyo rasuwar mutane fiye da 100.