Microsoft ya soma karbar kwandalolin bitcoins

Hakkin mallakar hoto AFP

Microsoft ya soma karbar biya ta hanyar amfani da kwandalolin bitcoins

Za a iya amfani da kudin yanzu a asusun Microsoft ta hanyar sayen abubuwa da dama da kamfanin Microfost din ke yi.

Za a iya amfani da kudin na bitcoins wajen sayen kayan wasan yara da wasu manhajojin wayoyi ko kuma domin sayen manhajar microsoft.

Microsoft shi ne kamfani na baya bayannan cikin manyan kamfanoni da zai yi mu'amala da kwandalolin bitcoins.

Microsoft dai bai yi wata sanarwa ba a hukumance game da matakin da ya dauka na marawa bitcoins baya, sai dai ya kara wani shafi a shafukan da yake mua'amala da kwastomominsa inda ya yi bayani game da yadda za a iya amfani da kudin wajen yin ciniki a kamfanin

A yanzu haka dai ana iya amfani ne da kwandalolin bitcoins ne a Amurka kadai.