An bukaci kasashen Afrika su fice daga ICC

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mista Museven ya ce kotun ICC ta zama kafa ta danniya ga Afrika

Shugaban kasar Uganda ya yi kira ga daukacin kasashen Afirka da su fice daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC, wacce ya ce an mai da ita wata kafa ta danniya ga nahiyar.

A cewar Yoweri Museveni, ICC kotun kasashen Yamma ce, kuma zai gabatar da wata shawarar ficewa gaba daya a taron Kungiyar Tarayyar Afirka na gaba.

Mista Museveni ya fadi hakan ne bayan da kotun ta janye tuhume-tuhumen aikata laifukan cin zarafin bil-Adama da ake yi wa shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, amma ta ci gaba da tuhumar mataimakinsa, William Ruto.

Ya kuma ce bai dace ba a tuhumi shugabannin kasashen Afirka ko mataimakansu.