'Yar aikin gida a Uganda za ta iay shan dauri

Image caption Jolly Tumuhirwe za ta iya shafe shekaru biyar a kurkuku

An samu wata 'yar aikin gida a Uganda da laifin cin zarafi.

'Yar aikin gidan, Jolly Tumuhirwe, wacce aka nadi bidiyonta tana duka tana kuma tattaka wata karamar yarinya da aka bar mata riko, ta shaida wa kotu cewa,ba komai ne ya harzuka ta ta daki yarinyar ba, illa dukan da mahaifiyar yarinyar ta sha yi mata a lokuta da dama.

Mahaifiyar yarinyar dai ta musanta hakan.

Wakiliyar BBC Catherine Byaruhanga ta ce " A ranar Litinin za a yanke wa Jolly Tumuhaire hukuncin da ka iya kaiwa ga zaman kaso har na tsawon shekaru biyar."