Ana ci gaba da jiran sunan mataimakin Buhari

Nigeria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nan ba da jimawa ake sa ran jam'iyar ta APC za ta bayyana sunan mataimakin Buhari

A jiya juma'a shugabannin jam'iyar ta APC sun kwashe tsawon lokaci suna tattaunawa a bayan fage domin zaban wanda ya fi cancanta.

Bayanai da dama daga Najeriyar na nuni da cewa akwai alamun jam'iyar za ta zabi gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi yayin da wasu a 'ya'yan jam'iyar ke nuna bukatar a zabi gwamnan jihar Legas Babatunde Raji Fashola.

Ana kuma sa ran nan ba da jimawa ba jam'iyar ta APC za ta bayyana zabin da ta yi yayin da tuni Shugaba Jonathan ya bayyana mataimakinsa Namadi Sambo a matsayin wanda zai ci ga da tafiya da shi.

Wannan na zuwa ne bayan zaben fitar da gwanin da jam'iyyar ta APC ta kammala ranar Alhamis, inda Janar Buharin ya lashe kuri'u 3,430.

Gwamnan Kano, Rabi'u Kwankwaso ya zo na biyu da kuri'u 974, yayin da tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar ya zo na uku da kuri'u 954.

Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya samu 674, yayin da mawallafin jaridar Leadership, Sam Nda Isiah ya samu kuri'u 10.