Bolivia za ta rage Jami'an tsaro masu teba

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Teba ta yi wa sojoji da 'yan sandan Bolivia yawa

Rundunonin soji dana 'yan sanda a kasar Bolivia sun soma daukar sunayen mambobinsu masu tsabar kiba bayan da Shugaban kasar ya yi korafin cewa mafiyawancinsu kibar su ta baci.

Kafafen yada labaran Bolivia sun ambato jami'an sojoji su na cewa za a tattara bayanan ne a lokacin jarrabawar kwarewar da za a yi wa 'yansanda da sojojin ta gaba, a wani bangare na wani shiri da nufin daidaita kirar jikinsu.

An kuma haramtawa 'yan sanda da sojoji sanya kakinsu, har sai an ga cewar jikinsu ya komo daidai yadda ake bukata, ta yadda kakin zai zauna tsaf a jikinsu.

Gwamnatin kasar dai na samarwa 'yan sanda da sojojin kasar kayayyakin wasanni, bayanda sojojin su ka yi korafin cewa basu da kayayyakin motsa jikin da zai sa jikinsu ya yi kyau.