Za a bullo da manhajar lasisin tuki

Hakkin mallakar hoto iowa
Image caption A cikin shekarar mai zuwa ne za a fara gwada aiki da manhajar lasisin tuki ta wayar salula

Jihar Iowa ta kasar Amurka tana kokarin bullo da wata manhajar wayar salula da direbobi za su rika nuna lasisinsu na tuki da ita.

Jami'ai a jihar suka ce manhajar zata rika amfani da lambobin sirri da bayanan halittar mutane domin tantance wadanda zasu rika amfani da ita.

Gwamna Terry Branstand ya ce "lallai mun yi nisa a kan wannan shirin".

Ma'aikatar sufuri ta jihar Iowa ta ce a cikin shekara mai zuwa ne za a fara gwada aiki da manhajar.

Za a rika amfani da manhajar ce a wuraren duba ababen hawa, da wurin jami'an tsaro, da kuma filayen jiragen sama na Iowa.

Jihar Iowa tana daga cikin jihohi 30 da suka amince direbobi su rika nuna shedar inshorar ababen hawansu ta na'urorin kwamfuta.

Ma'aikatar sufurin ta ce mazanua jihar ta Iowa za su ci gaba da yin amfani da katin lasisin tuki da suka saba amfani da shi.