Wajibi ne gwamnati ta kare rayukan jama'a - Bishop Kwashi

Jos Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bishop Kwashi ya ce hakkin gwamnati ne ta kare jama'rta

A Nijeriya, ana ci gaba da maida martani game da harin tagwayen bama-bamai da suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da talatin da kuma wasu kusan hamsin suka jikkata, a birnin Jos na jihar Filato, a yammacin Alhamis.

Babban Bishop na Darikar Angalika a Yankin na birnin Jos, Archbishop Benjamin Kwashi, ya ce wajibi ne gwamnatin Nijeriya ta nuna cewa lallai za ta iya kare rayukan talakawan kasar, yayin da matsalar tsaro ke kara ta'azzara.

A cewar Bishop Kwashi akwai mutanen da suke amfani da "rigar addini" domin su haddasa husuma a tsakanin al'umar jihar Filato dama Nijeriya baki daya.

"Akwai wadansu na hanun iblis da suka dauki ragamar rigar addini amma ko ba addini bane munafarsu daban ne, to yanzu mun gane."

Yanzu haka gwamnatin Jihar ta dora alhakin hare-haren akan kungiyar nan ta Boko Haram mai tada kayar baya.