'Ba jama`a sosai a Mubi'

Garin Mubi Hakkin mallakar hoto Unidentified Journalist

Rahotanni daga garin Mubi da ke jihar Adama a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya na cewa mazauna garin sun fara komawa gida.

A 'yan makwannin da suka gabata jami'in tsaro da hadin-gwiwar maharba suka kwace garin daga hannun 'yan kungiyar boko haram.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Mai martaba Sarkin Mubi, Alhaji Abubakar Isah Ahmadu ya koma fadarsa.

Sai dai rahotanni na cewa garin na fama da matsaloli, musamman ma ta fuskar kiwon lafiya.

Sakataren Fadar sarkin Mubi, Alhaji Yerima Tijjani ya tabbatar wa BBC cewa jami'n kiwon lafiya ba su koma bakin aiki ba.

Kuma a cewarsa, har yanzu mafi yawan al'umar garin ba su koma gida ba, duk da cewa jami'an tsaro da hadin-gwiwar maharba da 'yan kato-da-gora na ci gaba da kare garin Mubi da kewayensa.