Mu ci gaba da zuba jari-OPEC

Shugaban kungiyar kasashe masu arzikin mai, wato OPEC , Abdallah Al-Badri ya yi kira ga kasahen Larabawa da su ci gaba da saka jari a harkar hako mai duk da faduwar farashin da aka samu.

Ya ce saboda muguwar faduwar da farashin mai ya yi, ya kamata a ci gaba da saka jari saboda kada a samu karancinsa idan wata rana farashin ya sake tashi.

Al-badri yana magana ne a karon farko tun bayan da OPEC ta yanke shawarar cewa ba za ta kara yawan man da take fitarwa ba.

Farsashin gangar man dai bai kai dala sittin ba ko da aka rufe kasuwarsa a yammacin Juma'a.