'PDP ba ta fuskantar barazanar wargajewa'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan takara da dama a Jam'iyyar PDP sun bayyana rashin gamsuwa da zabukan fitar da gwani

Ministan babban birnin tarayyar Abuja Sanata Bala Muhammad ya ce jam'iyyarsu ta PDP ba ta fuskantar barazanar darewa duk kuwa da irin rigingimun da suka biyo bayan zabukan ta na fitar da gwani.

Senator Bala Muhammad ya yi watsi da maganganun da wasu ke yi na cewa jam'iyyar PDP ta dauko hanyar wargajewa.

Ministan Abujan ya ce 'babu inda zaben tantancewa bai raba mutane ba, su ma jam'iyyar adawa haka ne'

Ya kara da cewa abubuwan da suka faru sun biyo bayan yadda jama'a da dama ke son tsayawa takara ne a jam'iyyar.

Zabukan fitar da gwani da jam'iyyar ta gudanar dai a matakai daban daban sun bar baya da kura.