Dubban jama'a na zanga-zanga a Amurka

Dubun dubatar jama'a daga kungiyoyin farar-hula ne ke zanga-zangar a Washington DC, sakamakon kashen-kashen bakar-fata da 'yan sanda ke yi a Amurka .

Hatta dangin bakar-fatar nan da aka halaka a Misouri da ke jihar Ferguson, wato Micheal Brown, ana sa ran cewa za su shiga cikin wannan zanga-zangar.

Kuma ana kyautata zaton cewa za a yi wannan zanga-zangar a birnin Newyork da wasu birane masu yawa.

Babban abin da ke fusata jama'a shi ne hukuncin da wani wani babban Alkali ya yanke cewa ba za sauya 'yan sanda ba, duk kuwa da yadda mace-macen bakar fatar ke kara ta da hankali a Amurka baki daya.

Manufar zanga-zangar dai ita ce jan hanakalin mahukunta zuwa ga wannan matsala ta kisan bakar-fata ba gaira-ba-sabar.

Reverend Charles E Williams na kungiyar National Action Network ya ce sun fito ne kwansu da kwarkwata don nuna fushinsu game da yadda Alkalai ke wanke 'yan sanda bayan sun halaka bakar fata.

A ranar 9 ga watan Agustan da ya wuce ne wani dan sanda ya kashe Micheal Brown a wani artabu a Ferguson.

Kazalika, Mr Garner shi ma 'yan sanda sun masa sanadi a watan Yuli a wata kokawar danne shi, lokacin aka zarge shi da sayar da taba a kan titi.

Wani abin da ya kara daga wa jama'a hankali shi ne yadda wani hoton bidiyo ya nuna lokacin da yake koka wa 'yan sanda cewa ba ya iya numfashi, kuma wannan ne ya zame masa sanadi.