Ana ci gaba da zanga zanga a Amurka

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Masu zanga zangar suna so a kawo karshen nuna wariyar launin fata

Dubban mutane a Amurka sun cigaba da zarga-zangar nuna fushi game da kisan da 'yan sanda suka yiwa wasu bakaken fata a kasar.

Masu zanga-zangar wadanda suka hada da farare da bakaken fata, sun yi takkaki a biranen Washington da New York, da Boston da dai sauransu.

Dayawa daga cikinsu suna dauke da kwalaye masu dauke da rubuce rubuce kamar "Rayuwar Bakaken fata tana da muhimmanci" da kuma "'yan sanda ku daina nuna wariyar launin fata".

Masu zanga zangar suna bukatar shugabannin siyasa a Amurka su saurari bukatunsu na so a kawo karshen nuna wariyar launin fata.

Sun ce "muna kira a ga 'yan siyasar Amurka su tabbatar da kare rayukanmu, dana 'ya'yan, sannan a rika mutunta mu kamar yadda ake ma kowa".