Shugabannin ECOWAS na taro kan tsaro

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Taron na Abuja shi ne zai kasance na 46

Najeriya na daukar bakuncin taron shugabannin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO a Abuja, babban birnin kasar.

Taron wanda za a kwashe yinin ranar Litinin ana yi, zai duba batutuwa ne da dama da suka shafi tsaro da na siyasa a yankin.

Kungiyar Boko Haram na ci gaba da zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da ma wasu kasashe makwabtanta da ke yankin na Yammacin Afrika.

Haka kuma taron zai duba matsayin ECOWAS kan Burkina Faso, wadda ke karkashin mulkin wucin-gadi.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai gabatar da jawabi na musamman, kafin takwarorinsa su shiga tattaunawa a asirce.