An bukaci a yafe ma kasashe masu ebola bashi.

barnar cutar ebola a Guinea Hakkin mallakar hoto
Image caption barnar cutar ebola a Guinea

Wani rahoto na majalisar dinkin duniya ya yi kira ga masu bin bashi na duniya da su soke basussukan da suke bin kasashen nan guda uku da cutar Ebola ta yi wa mummunan barna.

Rahoton, wanda ya fito daga hukumar tattalin arziki na Afrika a majalisar dinkin duniya UNECA ya kara da cewa annobar ta yi gagarumin tasiri kwarai kan tattalin arziki, da durkusar da harkokin yawon bude ido da bangaren zuba jari, da harkokin jama'a da kuma samar da ayyukan yi.

Mr Dimitri Sanga, daya daga cikin wadanda suka yi aiki a kan rahoton na hukumar ta UNECA, ya ce sauke nauyin bashin zai saukakawa kasashe ukun tare da basu damar sake tsayawa da kafafunsu. Ya ce hakan zai ba su damar amfani da kudaden da suke kashewa wajen yaki da cutar ta ebola domin ayyukan ci gaban kasa.