Google ya kwashe injiniyoyi daga Rasha

Babban Daraktan Kamfanin Google Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Babban Daraktan Kamfanin Google

Kamfanin sadarwa ta Internet Google ya tabbatar da rahotannin dake cewar ya yi shirin kwashe Injiniyoyinsa daga kasar Rasha.

Kamfanin yace, yana nan "kan bakansa" na yin maraba da masu aiki da shafinsa a Rashar, ya kuma gaya ma BBC cewar ya taba kwashe injiniyoyinsa daga wasu kasashe a wasu lokutta.

Kamfanin Google ya ki fadin ko ma'aikata ne wannan janyewar za ta shafa.

A cikin watan Yulin wannan shekarar, majalisar dokokin Rasha ta zartas da wata doka wadda ta nemi kamfanonin sadarwa na Internet ta rinka adana bayanai na sirri na mutane a cikin kasar.

Fadar gwamnatin Rasha ta ce dokar, an shirya ta ne ta kara karfafa yadda za a kare bayanai nba mutane, to amma masu sukar lamiri suna kallon wannan a matsayin wani yunkuri na tace hanyoyin shiga Internet, saboda dokar za ta baiwa gwamnati ikon toshe shafukkan internet wadanda suka ki aiki da dokar.

Kamfanonin sadarwa na Internet suna adana bayanai a wasu shirga-shirgan ma'adanar bayanai a duniya, kuma ba su alakanta ma'adanar wadannan bayanai da yankin da mai bayanan yake. Ma'ana yawanci ba a ajiye bayanan mai mu'amalla da internet a kasar sa.

A cewar jaridar da ake bugawa a Wall Street, kamfanin na Google dai zai bar wasu ma'aikatan da suka hada da masu kula da huddar tallace-tallace da wasu 'yan ma'aikatan da za su taimaka musu a Ofishin na Rasha.

A cikin wata sanarwa, kamfanin ya fada cewar, sun dauki abokan huddarsu a Rasha da mutunci, don haka yana da ma'aikata da za su taimaka mu su.

Karin bayani