Nijar na neman tallafi don 'yan Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumomin sun ce suna sa ran yawan 'yan gudun hijrar ya kai dubu 150

Gwamnatin Nijar na neman taimakon domin tallafa wa dubban yan gudun hijirar Najeriya da ke cikin jahar Difa wadanda suka gudo saboda 'yan Boko Haram.

Gwamnatin ta ce tana bukatar dala biliyan 17 na cfa ta kasar domin sama wa yan gudun hijirar da ma yan asalin yankin na Difa da ke cikin matsatsi kayayyakin abinci da sauran abubuwan more rayuwa.

Hukumomin Nijar din sun ce a da mutanen na Difa ne ke taimaka wa mutanen, amma a yanzu, lamarin ya fi karfinsu, su ma suna bukatar taimako.

'Yan gudun hijirar sun wuce dubu 87, kuma kusan dubu 40 duk yara ne.