An fara wahalar man fetur a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A shekarar 2012 gwamnati ta kara farashin fetur, lamarin da ya janyo zanga-zanga

Jihohi da dama a Najeriya sun fara fuskantar wahalar man fetur tun daga karshen makon jiya.

Rahotanni na cewa hakan na faruwa ne sakamakon jayin aikin da kungiyoyin ma'aikatan man fetur da iskar gas suka fara ranar Litinin.

Yanzu haka dai layukan motoci da sauran abubuwan hawa sun cika kusan kowanne gidan sayar da mai a Abuja, babban birnin kasar.

Kazalika, rahotannin da muka samu daga jihohi da dama na cewa ana fama da karancin man, kuma ana sayar da shi sama da farashin da aka kayyade.

Kusan kowacce shekara dai sai an yi fama da wahalar man fetur a kasarta Najeriya, musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

A lokacin bikin sabuwar shekarar 2012 ne shugaban kasar, Goodluck Jonathan ya kara farashin man fetur, lamarin da ya jawo zanga-zanga a kowane sashe na kasar.

Najeriya dai ita ce kasa ta shida mafiya arzikin man fetur, sai dai duk da haka 'yan kasar na fama da matsanancin talauci.