NNPC na tattaunawa da ma'aikata kan yajin aiki.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministar harkokin man fetur a Nigeria, Diezani Alison- Madueke

Babban kamfanin mai na Nigeria, NNPC , ya ce yana tattaunawa da kungiyoyin kwadago na fannin man kasar wato PENGASSAN DA NUPENG kan yajin aikin da suke yi.

Kamfanin na NNPC ya ce yajin aikin bai kamata ya jefa jama'a cikin halin ha'ula'i ba, domin kungiyoyin na nuna fushi ne a matakin da wasu kamfanoni na kasashen waje suka dauka kan ma'aikatansu.

Kungiyoyin sun gabatar wa gwamnati jerin wasu bukatu wadanda su ke so a biya musu ko kuma ba za su koma aiki ba.

A cewarsu gwamnati ta bar matatun man kasar sun lalace babu gyara, sannan kuma titunan kasar sun lalace abinda ke janyo tsaiko wajen jigilar mai a shiyoyin kasar.

Kungiyoyin kuma sun bukaci gwamnati ta rage farashin man fetur sannan kuma sun yi korafin cewa an ki amincewa da kudurin doka da zai yi garan bawul ga bangaren man fetur na kasar.