An kirkiro shafin Pirate Bay bayan rufe shi

Hakkin mallakar hoto Isohunt
Image caption Sabon shafin an ce kwaikwayon Pirate Bay ne

Shafin Isohunt da ke samar da damar bude abubuwan da aka yi kwaikwayon su, ya kirkiri shafin abokin hamayyarsa, Pirate Bay, bayan an rufe shi a makon da ya wuce.

Kirkirarren shafin yana kan intanet kuma yana aiki sosai kamar yadda masu amfani da shi suka tabbatar.

Tun a makon da ya wuce ne aka rufe shafin Pirate Bay, daya daga cikin shafukan da aka fi ziyarta, a yayin wani farmaki da 'yan sanda suka kai a Sweden.

Isohunt, wanda aka haramta a Birtaniya a watan da ya wuce, ya ce ya yi kirkirar ne, domin kare 'yancin yada bayanai a intanet.

Isohunt ya ce idan aka dawo da Pirate Bay, zai rufe shafin da ya kirkira na Pirate Bay din.

Shi dai Pirate Bay yana samar da hanyoyin samun abubuwa da dama da aka kwaikwaya, kamar fina-finai da kade-kade da shirye-shiryen talabijin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutumin da ya kirkiro Pirate Bay

A makon da ya wuce ne 'yan sandan Sweden suka kai wani farmaki a kusa da Stockholm, inda suka kwace kayayyakin samar da intanet daga Pirate Bay, sakamakon bincike na shekaru.

Duk da cewa an kama wadanda suka kirkiri shafin da laifin satar fasaha, kuma an daure wasunsu, har yanzu an kasa rufe shafin dun-dun-dun.

A shekara ta 2012 Pirate Bay ya sauya tsarinsa yadda za a iya samunsa cikin sauki da kuma kwaikwayonsa a saukake.