Ana ci gaba da garkuwa da mutane a Sydney

Image caption Kawo yanzu ba a san wadanda ake garkuwa da su ba a yankin

'Yan sanda a birnin Sydney na Australia na ci gaba da killace wata anguwa da ake yawan hada-hadar kudi a cikin ta, inda wani dan bindiga ke garkuwa da mutane a wani kantin shan shayi.

Ana can ana ci gaba da tattaunawa da mutumin da ya yi garkuwa da mutanen, wanda 'yan sanda ke cewa sun san shi.

Biyar daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su sun kubuta, yayinda daruruwan 'yan sanda dauke da makamai suka yi ma ginin da ke titin Martin Place kawanya.

An saka wata bakar tuta da rubutun larabci da ke nuna alamun shahada a jikin tagar shagon shayin.

Fira ministan Australia, Tony Abbott ya ce akwai alamun batun na da nasaba da siyasa.