An daure 'yar aiki shekaru hudu a Uganda

Image caption 'Yan sanda a Uganda sun ba da shawarar ayi bincike sosai kafin mutum ya dauki mai reno ko 'yar aiki

Wata mata 'yar aikin gida a Uganda za ta shafe shekaru hudu a kurkuku bayan samunta da laifin cin zarafin karamar yarinyar da take kula da ita.

An dauki hoton bidiyon Jolly Tumuhirwe mai shekaru 22, tana dukan yarinyar 'yar watanni 18 tare da tattaka ta.

A ranar Juma'ar da ta wuce ne dai 'yar aikin ta ce ta daki karamar yarinyar ne saboda mahaifiyarta ta dake ta, zargin da uwar yarinyar ta musanta.

Mai shari'a Lillian Buchan ta shaida wa Jolly cewa ta aikata "babban laifin da bata da wata hujjar aikata shi", kuma ta yanke mata hukuncin ne saboda rashin imanin da ta nuna wa 'yar karamar yarinyar da bata san komai ba.