Netherland za ta ci Google tarar £12m

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Google na fuskantar kalubale

An yi wa kamfanin Google barazanar cin sa tarar kudi fam miliyan goma sha-biyu {£12m} muddin bai dauki matakan da suka dace ba na kare sirrin mutanen kasar Netherlands.

Hukumar kare bayanan sirri ta 'yan Dutch din ce ta yi wannan barazanar, wadda tace kamfanin na Google ya karya dokokin kasar a kan abinda zai yi da bayanan masu mu'amalla da shi.

An baiwa Kamfanin na Google wa'adin zuwa karshen watan Febrairu na shekara ta 2015 ya canza yadda yake ajiye bayanan sirri na mutane.

Kamfanin na Google ya ce kalaman na hukumar ta Netherlands, sun ba shi kunya.

Shugaban hukumar ta Dutch Jacob Kohnstamm ya gaya ma kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar wannan lamari na gudana ne tun a shekara ta 2012, kuma yana fata ba za a kure hakurinsu ba.

Jayayyar ta taso ne daga yadda kamfanin Google ke hada bayanai dangane da abinda mutane suka yi a shafin Internet ta yadda zai rinka tallace-tallace a kan abinda yake ganin suna da sha'awa a kan sa.

Kamfanin na Google ya yi amfani da bayanai da suka kama daga bayanan da mutum ya nema da sakonni na email da aka tura masa da wurinda ya samu bayanan da yake nema da irin hoton bidiyon da ya kan kalla a Internet wajen tattara bayanai na miliyoyin masu mu'amalla da shafin sa.

Dokokin na kasar Netherlands sun ce kamata ya yi kamfanin na Google ya sheida mutane cewar yana tattara bayanai game da su tare da neman iznin su kafin ya tattara bayanan da kiyasi kan su a cewar Mr KohnstamM.

Wani wakilin kamfanin Google ya ce "wannan umurni na hukumar ta Dutch ya kunyatar da mu, musamman kamar yadda muka gudanar da sauye-sauye da dama ga manufofinmu na kare bayanan sirri na mutane, daga damuwar da suke nunawa.

Yace, "sai dai kuma a baya-bayan nan mun tattauna wasu shawarwari na karin wasu sauyre-sauye da hukumar kare bayanan sirri ta Tarayyar Turai, muna kuma sa ido muna jiran lokacinda za ,mu tattauna a kan su nan ba da jimawa ba."

Karin bayani