Rikicin manoma da makiyay ya haddasa mutuwar mutane a Giwa.

Fulani makiyaya
Image caption Fulani makiyaya

A Jahar Kaduna kimanin mutane hudu ne suka rasu, wasu da dama kuma suka sami raunuka a yayin da wani rikici ya barke tsakanin Fulani makiyaya da manoma a karamar hukumar Giwa ta arewacin jahar.

Rahotanni na nuna cewa makiyayan na wucewa ne ta wani yankin karamar hukumar tare da Shanun su kimanin 2,000, wasun su kuma suka fantsama cikin gonaki, hakan ne kuma ya haifar da rikicin da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabatar da aukuwar lamarin, ta kuma ce an kama wasu mutane da ake dangantawa da rikicin.