Farashin man fetur ya yi kasa warwas

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Farashin man dai ya fadi zuwa kusan rabin kudin da ake sayen gangar mai tun daga watan Yuni.

Farashin danyen man fetur ya yi faruwar da bai taba yi ba cikin shekaru biyar da suka wuce.

Farashin mai samfurin Brent Crude ya fadi zuwa dala 59 a kan kowacce gangar mai daya.

Masu sharhi sun ce hakan ya faru ne saboda kasashe maso tasowa sun kara yawan man da suke hakowa, yayin da kasashen da ke sayensa suka rage man da suke saya.

Farashin man dai ya fadi zuwa kusan rabin kudin da ake sayen gangar mai tun daga watan Yuni.