Shekau ya yi wa sarkin Kano martani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau ya kuma soki sauran kungiyoyin musulunci da cewa kafirai ne

Kungiyar Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo inda shugabanta Abubakar Shekau ke mayar da martani ga sarkin Kano game da kiran cewa jama'a su tashi su kare kansu daga hare-haren kungiyar.

A bidiyon mai tsawon kusan minti 20, Abubakar Shekau, ya yi jawabi na sama da minti 16 cikin Larabci da Hausa da kuma harshen Kanuri, inda ya ke cewa sarkin Kanon Muhammadu Sanusi na biyu ya makaro da wannan kira.

A kwanakin baya ne sarkin kanon ya yi kira ga jama'a da suka hada da 'yan tauri cewa su tashi tsaye su kare kansu daga ayyukan kungiyar.

Bayan kalaman na sarkin ne aka kai hari mafi muni a jihar, a masallacin kofar gidan sarkin lokacin sallar Juma'a, a kawanakin baya, harin da ya hallaka mutane sama da dari daya da jikkata wasu da dama.