Al'ummar Nijar na bikin ranar Jamhuriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jami'an tsaro za su nuna hikimominsu daban-daban a lokacin bikin

Al'ummar Nijar na bukukuwan zagayowar ranar da kasar ta zama Jamhuriya, inda birnin Doso ke karbar bakuncin taron na bana.

Shugaban kasar Alhaji Mahamadou Issoufou ne zai jagoranci shagulgula da dama da za a yi na ranar.

A shekara ta 2006 ne tsohon shugaban kasar Tanja Mamadou ya kirkiro da shirin gudanar da shagulgulan sallar ta 18 ga watan na Disamba daga jiha zuwa jiha.

Yayi hakan ne da nufin samar da abubuwan raya kasa ga kowace jiha, daya bayan daya.