Simintin Dangote ya kara farashi a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dillalan na korafin cewa masu saya zasu yi zaton su suka sa kamfanin ya kara farashi

Dillalan da ke sayar da siminti a Nigeria sun koka kan tashin farashin siminti dare daya da kamfanonin sarrafa siminti a kasar.

Sun ce rashin sanar da su game da karin farashin da kamfanin Dangote bai yi ba tun da wuri na shafar kasuwancinsu.

Makonni biyu da suka wuce ne dai kamfanin na Dangote ya sanar da rage farashin siminti a kasar zuwa N1,000, amma yanzu ana sayar da buhu naira 1,450.

Wasu masana a Najeriyar na ganin tashin farashin baya rasa nasaba da rage darajar naira da babban bankin kasar ya yi.