Ebola: Saliyo za ta yi bincike gida-gida

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Saliyo na cikin kasashen da cutar Ebolar ta fi shafa a Afrika ta Yamma, inda ta kashe mutane 6,800

Hukumomi a kasar Saliyo sun sanar da shirin bi gida-gida a babban birnin kasar Freetown domin zakulo wadanda suka kamu da cutar Ebola.

Shugaba Ernest Bai Koroma ya kuma sanar da cewa za a daina kasuwanci ranar Lahadi, haka kuma za a takaita zirga-zirga tsakanin gundumomi.

Hakan ya zo ne bayan hukumomi a kasar sun haramta taron jama'a domin bukukuwan Kiristimeti da kuma na sabuwar shekara.

Wata sanarwar da shugaban ya fitar ta ce ana fatan binciken zai taimaka wajen karya lagon yadda cutar ke yaduwa.