Boko Haram ta kashe mutane 30 a Damboa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan Boko Haram sun kai harin ne ranar Lahadi amma sai yanzu labarin ke fitowa saboda rashin hanyoyin sadarwa.

Rahotanni daga kauyen Gumsuri da ke Damboa a jihar Bornon Najeriya na cewa 'yan Boko Haram sun kashe mutane da dama a harin da suka kai kauyen.

Mazauna kauyen sun ce 'yan Boko Haram din sun kuma sace mutane da yawa.

A cewarsu, mutanen da aka sace sun hada da maza da mata.

An kai harin ne tun ranar Lahadi amma sai yanzu aka samu labari saboda rashin hanyoyin sadarwa.

Har yanzu dai babu cikakken bayani game da adadin mutanen da aka kashe ko aka sace daga kauyen.

Jihar ta Borno dai na ci gaba da fuskantar hare-haren kungiyar ta Boko Haram, duk da cewa tana daga cikin jihohin da ke karkashin dokar ta-baci.