Dakarun Kamaru sun kashe 'yan Boko Haram 116

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru sun ce za su murkushe 'yan Boko Haram

Dakarun tsaron Kamaru sun ce sun hallaka 'yan Boko Haram 116 a yankin Amchide da ke lardin arewa mai nisa a cikin kasar.

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce 'yan Boko Haram sun kai harin a sansanin soji da ke Amchide a ranar Laraba, amma kuma sai dakarun kasar suka dakile harin suka kashe mayakan kungiyar da dama.

A cewar dakarun Kamaru, sakamakon tashin hankalin, 'yan Boko Haram sun lalata wasu motocin sojin kasar.

Sai dai a bangaren Kamaru, an hallaka soji daya sannan kuma soji daya ya bace.

A 'yan watannin nan, kungiyar Boko Haram ta kara karfi musamman a yankunan kan iyakar Nigeria da Kamaru inda ta hallaka mutane da dama.