Shin Jonathan zai yi kamfe a arewa maso gabas?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jonathan bai je jihohin arewa maso gabashin Najeriya inda ke fama da hare-haren Boko Haram a wannan shekarar ba

A Najeriya, yayin da manyan jam'iyyun kasar biyu suka fitar da 'yan takarar shugabancin kasasu, wani abu da za a mayar da hankali a kai shi ne zuwa yakin neman zabe.

Jam'iyyar PDP mai mulkin kasar dai ta sake tsayar da shugaba Goodluck Jonathan domin ya fafata da Janar Muhammadu Buhari, wanda jam'iyyar adawa ta APC ta tsayar.

Hukumar zaben kasar dai, INEC ta amince 'yan takara su yi yakin neman zabe daga yanzu har zuwa farkon watan Fabrairu, lokacin da za a fara kada kuri'a.

Wata tambaya da 'yan kasar ke yi ita ce: shin shugaba Jonathan zai je yakin neman zabe a yankin arewa maso gabashin kasar da ke fama da hare-haren 'yan Boko Haram?

Jonathan bai je yi wa mazauna yankin jaje ba

Dalilan wannan tambaya na da dama, amma babba daga cikinsu shi ne:

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jonathan na shan suka kan yaki da Boko Haram

Tunda 'yan Boko Haram suka karfafa kai hare-hare musamman a wannan shekarar, shugaban bai kai ziyarar jaje yanki ba.

Wannan mataki dai ya sa mazauna yankin na ganin shugaban bai damu da su ba, duk da yake ya kai ziyarar jaje a wasu yankunan kasar.

Ko da a lokacin da aka sace 'yan matan makarantar Chibok da ke jihar Borno su fiye da 200, shugaba Jonathan bai kai ziyara a yankin ba, lamarin da ya janyo masa suka daga ciki da wajen kasar.

Haka kuma masu sharhi na ganin shugaban ya gaza kawo karshen hare-haren da 'yan Boko Haram ke kai wa ne saboda 'yan adawa sun fi karfi a yankunan da ake kai hare-haren.

A hirarsa da BBC, mai bai wa shugaban shawara na musamman, Mr Doyin Okupe ya ce watakila ma dai shugaban ba zai kai ziyara a garin na Chibok ba, kodayake ya kara da cewa mai yiwuwa Mr Jonathan ya je yakin neman zabe a arewa maso gabashin kasar.

Yanzu dai mazauna yankin sun zuba idanu su gani ko shugaban zai je wajensu domin neman su kada masa kuri'a a zaben shekarar 2015.

Idan ya je, shin me zai gaya musu? Kuma wacce amsa za su ba shi?