Falasdinawa na neman 'yanci cikin shekaru uku

Benjamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto EPA

Isra'ila ta soki yunkurin Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya na shata wa'adin shekaru ga Isra'ila ta kawo karshen mamayar da ta yi wa yankunan Falasdinawa.

Falasdinawan sun gabatar da kudiri ne ga Kwamitin Tsaron majalisar.

Haka kuma kudurin ya ce ya kamata a sami yarjejeniyar zaman lafiya cikin shekara guda.

Falasdinawan suna son kafa kasa mai 'yancin kanta a gabacin birnin Kudus, da Gabatar Yammacin Kogin Jordan da Zirin Gaza, wadanda dukkansu Isra'ilar ta kama a yakin 1967.

Wani daftarin kuduri wanda kasar Jordan ta gabatar wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kiran a samar da wata yarjejeniya ta zaman lafiya a cikin shekara daya.

Firayiminstan Isra'ila ya ce kudurin ba zai sa a cim ma yarjejeniyar zaman lafiya cikin hanzari ba, inda ya ce babu abin da zai sauya ba tare da amincewar Isra'ila ba.