An cimma yarjejeniya game da yanayi a Lima

Wakilai a taron yanayi a Peru Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wakilai a taron yanayi a Peru

Wakilai a Majalisar Dinkin Duniya sun cimma yarjejeniya dangane da yadda kasashe za su bullo ma sauyin yanayi.

Wakilan sun amince da wani tsari na neman kasashe su zayyana matakan da kasashensu za su yi alkawarin cikawa, su kuma gabatar da su a taron koli da za a yi a badi.

Bambance-bambancen ra'ayoyi a kan daftarin yarjejeniyar a tattaunawar ta makonni biyu da aka yi a Lima, sai da suka tsawaita taron da kwanaki biyu.

Kungiyoyin masu kare muhalli sun ce yarjejeniyar ba tsayayyar manufa ba ce da aka cimma, to amma Tarayyar Turai ta ce wani taki ne ta fuskar cimma yarjejeniya kan batutuwan da suka shafi kariyar muhalli a taron da za a yi a badi a birnin Paris.

An yi ta kai ruwa rana a tattaunawar saboda rarrabuwar kawuna da aka samu tsakanin kasashe masu arziki da matalauta dangane da yadda za a dora ma kowacce kasa alhakin rage yawan hayaki mai gurbata yanayi.

An aiwatar da yarjejeniyar Tahe wasu sa'oi bayan kasashe masu tasowa sun yi watsi da daftarin kudurin da tun farko aka cimma yarjejeniya a kansa, saboda sukar da suke yi ma kasashe masu arziki ta rashin daukar alhakin da ya rataya a wuyan su na yaki da dumamar yanayin ta hanyar rage yawan hayaki mai dumama duniya da kuma biyan diyya kan sakamakon da hakan ya haifar.

Ministan Muhalli na Peru Manuel Pulgar-Vidal wanda ya jagoranci taron kolin, ya gaya ma manema labarai cewa "a matsayinsa na daftari, bai kammala ba, to amma ya kunshi matsayin dukkan kasashe."

Miguel Arias Canete Kwamishinan muhalli da makamashi na Tarayyar Turai ya ce Tarayyar Turai tana bukatar ganin an samu sakamako mai girman gaske, amma yace, har yanzu muna da imanin cewa "ana kan hanya ta amincewa da yarjejeniya ta duniya" a taron kolin da za a yi badi a birnin Paris.

Ministan sauyin muhalli na Tarayyar Turai Ed Davey ya ce "ba wai zance za a yi tafiya ba ne a filin yawon shakatawa na Paris."

Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wani muhimmin mataki a kokarin da ake yi na cimma yarjejeniya a birnin Paris.

Karin bayani