Apple ya nuna bacin rai game da binciken BBC

Image caption Ma'aikatan Apple su na runtsawa a bakin aiki

Apple ya ce ya yi matukar rashin jin dadi game da binciken da BBC ta gudanar akan yanayin da ma'aikata ke aiki a masana'antun dake samarwa da kamfanin kayayyaki.

Shirin na BBC Panorama ya shaida cewa ana take ka'idar aiki wajen sa'oin da ma'aikata suke dauka suna aiki da kuma wajen bayar da katin shaidar aiki da tarurrukan aiki.

A wani sakon email da kamfanin ya aikewa ma'aikatansa, babban jami'in kamfanin Jeff Williams ya ce bai san wani kamfanin da ya ke yin irin abubuwan da Apple yake yi ba, domin inganta yanayin aikin ma'aikata.

Amma sai dai ya kara da cewa: '' Muna iya yin fiye da haka.''

Editan shirin Panorama na BBC Ceri Thomas ya ce yana tsaye kai da fata akan aikin binciken da su ka yi.

Ya ce sun gano cewa yara kanana suna aiki a mahakar ma'adinin tin masu matukar hatsari a Bangka da kuma Indonesia

Yayinda Apple ya tabbatar da cewa da farkon wannan shekarar yana samun ma'adin tin din daga Bangka, sai dai jami'in ya ce ba a taba tabbatar da cewa ko haramtaccen ma'adin tin na shiga cikin abubuwan da ake samar musu ba

Apple dai tun farko ya ki amincewa ya yi hira da shirin na BBC.